Me ka ke nema?


Shafin Farko

Tashar Mariri



Ƙofar Gidan Sarkin Kano; Gidan Rumfa


Gabatarwa

Tasha ce da aka gina ta a cikin shekarar 1992, zamanin mulkin Arc Kabiru Ibrahim Gaya. Cinkoson motoci a Tashar Na’ibawa da kuma ƙoƙarin bunƙasa harkokin sufuri a jahar Kano ya saka aka gina wannan tasha.

Tasha ce da take a Kudu-maso-Gabashin garin Kano. Tana nan a Unguwar Mariri daga gefen Yamma da titin Wudil.

Tasha ce da take da yalwataccen sararin ajiye motoci. Ana ɗaukar jama’a zuwa garuruwan jahohin Yobe, Maiduguri, Bauchi, Gombe, Adamawa da kuma Taraba.

Dukkan garuruwan da ke kan hanyar Maiduguri idan ka wuce Azare ana samun motar zuwa garin a wannan tasha.

Garuruwa irin su Darazo, Dukku, Gombe, Kumo, Lafiyan Lamurde, Numan, Ngurore, Mubi, Jimeta, Yola har zuwa bakin iyakar Kamaru ta wannan hanyar ana samun motar zuwa garuruwan a tashar.

Hakan nan ma idan ka ɗauka daga Numan ka nufi Jalingo har zuwa Gembu akwai motar zuwa garuruwan a wannan tashar.

Sauran garuruwa irin su Biyu Damaturu, da sauransu, duk ana samun motar zuwa can a wannan tasha.

Manazarta:


Tattaunawa da Alhaji Ja’afar Abubakar Abdullahi Mariri, wanda aka fi sani da Khadimul Islam ɗin Kwankwasiyya a ranar Litinin 1 ga watan Janairun 2019.

Ziyarar gani da ido zuwa tashar.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub